Mai rikon kwarya na Jam’iyyar APC a Jahar Kano, kuma dan takarar kujerar shugabancin Jam’iyyar APC ta Kasa, Ahmad Mansir Aliyu Matawalle, bai cika sharudan zaben dake gudana a Kano ba. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Inda aka ce ba’a bi hanyoyin da aka tsara ba wajan zabar Dan takarar Ahmad Mansir Aliyu Matawalle ba.
Ahmad Mansir Aliyu Matawalle, yayi bakin cikin kan rashin sanya hannu da magoya bayan jam’iyyar sukeyi. Yace wannan rashin sanya hannun Yan jam’iyyar ya samo asalin ne wajan rashin bin ka’ida wajan zaben shugaban. Wanda hakan ya sabama tsarin dokar jam’iyyar.
KARANTA:- DA DUMI-DUMI: Manyan masu ba gwamna shawara sun koma APC
Ya bayyana hakane lokacin da yake zantawa da manema labarai a Tarauni, Karamar hukumar Tarauni dake Jahar Kano, inda aka gudanar da zaben.
Kamar yadda yace “Masu rikon kwarya sun sanar da gudanar da zaben kamar yadda Jam’iyyar ta tanada, an bayyana a kundi na 20 na tsarin jam’iyyar, ya bayyana cewa kowane dan jam’iyyar dole ya fito ya zabi shugaban sa, idan lokacin yayi a wannan mataki.”
“Idan ka lura mutane kadan ne suka fito wajan gudanar da zaben, wanda hakan ya sanya wasu sunyi nasarar dauke mukamin.”
“Kundin jam’iyyar yayi bayani yadda zaben zai kasance, Kuma muna da tsari.”
“Rashin bin tsarin dokar jam’iyyar ne, da kuma fushi da wasu Yan jam’iyyar sukayi ne ya janyo hakan.”
“Ina kira ga masu rikon kwarya na Kasa dana jahohi, dasu bi tsarin dokar jam’iyya idan ana son cigaban Jam’iyyar.”
“Kamar yadda Shugaban rikon kwarya na Jam’iyyar ta Kasa Gwamnan Yobe Mai-Mala Buni, ya bayyanawa manema labarai yace sama da mutane miliyan arba’in ne sukayi rijista da jam’iyyar a kasa, Amma idan kayi la’akari da mutanen da suka zo zaben basa da yawa.”
“Ina kira ga Yan jam’iyya mu fito gaba dayanmu mu nuna goyan bayanmu ga jam’iyyar mu, idan muna son mu cigaba da jindadin jam’iyyar, Kuma mu sami damar lashe zaben shekarar 2023 mai zuwa.” Kamar yadda Aliyu Matawallen ya bayyana.