Rikicin Manoma da Makiyaya: An Shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kafa Ma’aikatar Kiwo
Kwamitin sake fasalin kiwo na kasa ya ba da shawarar kafa Ma’aikatar kiwo da za ta kula da rikicin manoma da makiyaya a kasar nan.
Kwamitin wanda ya gabatar da shawararsa na sake fasalin sana’ar kiwo a kasar nan ga shugaban kasa Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Villa a Abuja a ranar Alhamis ya bayyana cewa akwai kiwo iri hudu a kasar nan.
A cewar Jagoran tawagar kuma shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace, akwai makiyayan da ke zaune a gida, akwai wadanda ‘yan Najeriya ne da ke kaura daga sassan kasar nan daban-daban, akwai makiyayan da suka fito daga makwabta wajen
Kasashen yammacin Afirka, da kuma waɗanda suka zauna a cikin wasu kabilun har suka zama ‘yan asalin yankin.
KARANTA NAN:An tsige shugaban wata Ƙaramar Hukuma a Najeriya akan Zargin karkatar da Kuɗi
Ganduje ya ce “Abin farin ciki ne da ya Jagoranci wannan tawaga wacce ta ƙunshi ‘yan Najeriya masu kishin kasa, da kwararru a fannoni daban-daban na rayuwar Ɗan Adam a gaban mai girma Shugaban ƙasa domin gabatar da rahoton taron kasa da aka gudanar kan sake fasalin kiwon dabbobi a Najeriya.
Rahoton ya fito ne biyo bayan bukatar da ke akwai na yin garambawul da bunkasa harkar kiwo da samar da hanyoyin magance rikice-rikicen da aka dade ana yi tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya.
An sha yin yunƙuri na bunƙasa sana’ar kiwo wanda ya samu tasgaro da kuma nasarori. Inganta harkar zai sanya makiyaya su samu wurin zama na din-din-din, gami da inganta harkar, amma saboda tsari da kuma ƙarancin kuɗaɗe haƙar bata cimma ruwa ba.
Rashin kasar da wadannan matsalolin ya haifar da yanayi marar kyau, wanda kuma yayi sanadiyyar haifar da tashin hankali a tsakanin manoma da makiyaya a fadin kasar nan.
Ya ce a yayin da Ganduje yale Gwamnan Jihar Kano, gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin zamanantar da kiwon dabbobi tare da karfafa wa kananan hukumomi gwiwa wajen tafiyar da alaka da mai kyau da sasanta rikice-rikicen da ke tsakanin kungiyoyin cikin lumana, don haka Jihar Kano ta ci gaba da zama a cikin Jihohin da suka fi zaman lafiya a tsawon shekaru takwas na mulkin shi.
Kwamitin da ya shirya wannan rahoto ya kunshi fitattun ‘yan Najeriya a ƙarƙashin Jagorancincin Farfesa Attahiru Jega tare da mambobin kungiyar masu zaman kansu da suka yi aikin kiwo da noma, wakilan kungiyoyin al’umma na manoma da makiyaya da kwararru a fannoni daban-daban na bunkasa kiwo da magance rikice-rikice.
Gwamna Ganduje ya ce aiwatar da shawarwarin za su kara habaka noma da kiwo da kuma inganta yanayin kiyaye muhalli da magance matsalolin da ke haifar da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da kuma taimakawa wajen rage tsadar fitar da dabbobi da madarar Shanu da makamantansu.