Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya gana da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP, tare da hasashen matakin da zai dauka na gaba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa hakan ya biyo bayan kuri’ar amincewa da kwamitin zartarwa na kasa ya kada kan amincewa da shugabancin Sanata Iyorchia Ayu.
Wike da masu goyon bayansa sun bukaci Ayu ya yi murabus a matsayin wani sharadi na zaman lafiyar jam’iyyar.
KARANTA ANAN: Gombe: Mamaye Ofishinmu Neman Rigima Ne Da Nuna Karaya – PDP
Sai dai alamu sun bayyana, a jiya, cewa shugabannin jam’iyyar PDP na yankin Kudu-maso-Yamma na yin taro a Ibadan, jihar Oyo, domin ingiza shiyyar wajen samar da shugaban jam’iyyar na kasa.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose; Shugabannin jam’iyyar PDP na jihohi da sauran shugabannin jam’iyyar na daga cikin wadanda suka halarci taron sirrin.
Taron dai a cewar majiyoyin jam’iyyar da dama, ya mayar da hankali ga tattauna makomar jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso Yamma da kuma ziyarar Atiku a jihohin Legas da Oyo.
Yayin da wata majiya ta shaida wa Vanguard cewa Makinde da sauran shugabannin jam’iyyar na iya kauracewa ziyarar Atiku, wata majiya kuma ta ce shugabannin na nan kan baka su cewa dole ne Ayu ya yi murabus domin share fagen samar da shugaban jam’iyyar na kasa daga yankin Kudu maso Yamma.
A wani labarin kuma: Rundunar Yan Sanda Ta Tabbatar Da Sace Wani Fasto Tare Da Neman Kudin Fansa
Rundunar ‘yan sanda a jihar Filato ta tabbatar da sace wani malamin addini, Rev. Bung Dong.
An yi garkuwa da Dong ne a kauyen Ganawuri da ke karamar hukumar Riyom a jihar.
DSP Alfred Alabo, jami’in hulda da jama’a na hukumar, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin a garin Jos.