Shugaban karamar hukumar Kafur dake jihar Katsina, Alhaji Garba Kanya, ya tabbatar da cewa ruwan sama mai karfin gaske tare da kankara ya lalata gonaki fiye da 300.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a wasu kauyuka takwas da ke yankin.
Shugaban ya shaida wa NAN a ranar Litinin a Katsina cewa ruwan sama mai karfi da kankara ya shafe sama da sa’o’i uku ya kuma shafi gonaki da gidaje a unguwannin Dutsen-Kura, Kanya da Gozaki.
KARANTA ANAN: Rikicin PDP: Makinde, Fayose, Wike Da Wasu Sun Gana A Ibadan
Al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Gidan Sabo, Kabalawa, Unguwar Tsamiya, Dandabo, Unguwar Maigarma, Unguwar Danwada, Unguwar Wanzamai da Unguwar Fulani.
Kanya ya ce amfanin gona da dama sun lalace da suka hada da Masara, Gero, Shinkafa, wake waken soya da kuma Barkono.
A cewarsa, amfanin gonakin da bala’in ya lalata ya kai na miliyoyin naira.
Kanya ya ce karamar hukumar ta kai rahoton lamarin ga hukumar bada agajin gaggawa ta jihar domin ta shiga cikin lamarin.
A wani labarin kuma: Gombe: Mamaye Ofishinmu Neman Rigima Ne Da Nuna Karaya – PDP
Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da mamaye ofishin yakin neman zabenta da ke jihar Gombe.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wasu da ake zargin magoya bayan jam’iyyar APC ne a jihar suka aiwatar da hakan.
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja, ranar Litinin.