Shugaban Bankin duniya ya ce mamayar Rasha a Ukraine ka iya durkusar da Tattalin arzikin duniya baki daya, yayin da farashin abinci, iskar gas da kuma daki sukayi tashin gwauron zabi.
David Malpass ya ce har yanzu kwai kasashen Turai da dama da suke dogaro da man fetur da iskar gas din kasar Rasha.
Kana ya ce kudurin Rasha na katse Bai wa nahiyar Turai gas zai kawo cikas da Tattalin azriki yankin.
Kazalika ya ce, tuni farashin albarkatun iskar gas ya yi tashin gwauron zabi a kasar Jamus guda daga cikin masu tattalin arziki.
Rasha da Ukraine na daga cikin manyan masu samar da taki da abinci , Malpass David , da yake magana jiya a Amurka , ya ce tuni kasashe masu tasowa ke fama da karancin abinci .
Comments 1