Mutum daya ya mutu yayin da wasu uku suka samu raunuka bayan wani gini ya rufta a yankin Woji na garin Fatakwal a jihar Rivers.
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya gano cewa, lamarin ya faru ne da yammacin jiya Laraba.
Daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, ya dora alhakin hakan a kan ruwan sama kaman da bakin kwarya da akasami a yankin aranar Talatar data gabata, wanda ya ce, ya shafi gine-gine da dama wadanda ba’a kammala ba.
Wanda abin ya rutsa da shi ya ce, mutum daya ya rasa ransa sanadiyar lamarin, yayin da wasu mutane uku suka samu mummunan raunuka daban -daban.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nayi sa’ar shiga harkar Fim, inji Fati Shu’uma
“Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a ranar Talata wanda ya shafi tubalin ginin, shi ne ya sa ginin ya rushe” inji shi.
“Ruwan ya yi tsanani sosai, kuma tuni ambaliyar ruwar ta sanya asarar dukiyoyi sosai a yankin” a cewar shi.
Kazalika ya ce, “Mutum daya ya mutu a lamarin, yayin da wasu mutane uku da suka samu raunuka, kuma an kwashe su zuwa asibiti domin duba lafiyar su,” in ji shi.
Wakilin jaridar Daily Trust yayi duk Mai yiwuwa wajan hi ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Rivers, SP Nnamdi Omoni game da lamarin, har zuwa lokacin hada rahoton Amma abun ya citira.