Rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato ta damke jami’inta da ake zargi da harbe matashi a jihar. Rundunar ta ce ta cafke shi ne domin gano dalilin da ya sa ya harbe matashin wanda yake dalibin jami’ar Jos ne.
Hakan ya fito ne a sanarwar da jami’in hulda da manema labarai na rundunar ta STF a jihar Filato, Manjo Ibrahim Shittu, ya fitar, inda ta ce ta samu rahoton ayyukan barayi da ‘yan kungiyar asiri a yankin Holshe a karamar hukumar Jos ta Kudu, musamman a lokacin da gwamnati ta sanya dokar hana fita don dakile yaduwar annobar korona.
Sun kuma ci gaba da cewa; jami’ansu sun kama matasa bakwai bisa bayanan da suka samu amma da suka gudanar da bincike sun gano cewa biyar daga cikinsu ba su da laifi sai suka sake su ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai sun ce kafin su kai ga fita daga harabar Hedikwatar ne jami’in soja a cikinsu ya harbe daya daga cikin matasan mai suna Rinji Bala akan cewa ya yi zaton za su gudu ne.