Jami’an hadaka na yankin Kudancin Afrika dake aikin kwantar da tarzoma a Mozambique sun hallaka Yan tada kayar baya 17 a wani samame da suka kai a Gundumar Cabo Delgado, bayan tarwatsa sansanin Yan bindigan a Chitama, kamar yadda suka bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Lahadi.
A samamen da rundunar da ake kira da Samim ta kai a Chitama ranar asabar din da tagabata, ya yi sanadiyar hallaka jami’in sojin ta guda, tare da raunata wasu da dama, kamar yadda sanarwar tace.
A cewar sanarwar a jiya Lahadi, jami’an hadaka sun yi bata kashi da wasu gungun Yan bindiga a Kudancin Kogin Messalo, inda nan take rundunar tayi nasarar kashe Dan bindiga guda, da kuma jikkata 3, tare da kwato kunshin alburusai, inda Kuma ta kama wasu Yan bindiga a raye.
Idan za’a iya tunawa a watan Yulin Shekarar nan ne, Kungiyar kasashen Samar da Cigaban yankin Kudancin Afrika SADC, ta amince da tura jami’an soji domin tallafawa takwarorin su na Mozambique, da zummar yakar yan tada kayar baya a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta Horas da Jami’an Civilian JTF 312 a Kaduna
Kasar Ruwanda ce ta fara tura jami’an soji guda 1,000, sai Botswana ta tura 296, yayin da kasar Afrika ta Kudu ta tura jami’an sojinta 1,500 zuwa Mozambique.
Kazalika Zambabwe ta tura da nata jami’an guda 304, domin su kara horas da takwarorin su na Mozambique a fannin yaki da Yan tada kayar baya.
Comments 1