• Sojin da ke ai ki akan hanyar Mokwa zuwa Jebba ne su ka ma wanda ake zargin.
•An kama wanda ake zargin sanye da kayan sarki da takalmar soji.
• An kuma bikawa rundunar yan sandan shi domin cigaba da gudanar da bincike akan wanda ake zargin.
Jami’an sojin kasar kasan nan dake ai ki a kan hanyar Mokwa zuwaJebba sun kama wani da ake zargin dan bindiga ne, lokacin da suke wani bincen kwa-kwaf a kan hanyar.
Hanyar dai, ta Mokwa zuwa Jebba, ta kasan ce hanyar da matafiyan da ke garin Abuja, jihar Ilorin da kuma Kwara ke amfani da ita yau da kullun.
Mai magana da yawun rundunar soji ta kasa Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana wannan nasaran inda ya ce, “an kama wadanda ake zargin ne a cikin wata mota, da musalin karfe 9 na dare, a kan haryar shi ta zuwa birnin Badun na jihar Oyo daga garin Zuru.”
Inda jami’an sojin suka tsare motar wanda ya yi ikirarin cewa, shi soja ne mai suna Sajen Aminu Sule, ko da jami’an suka tsanan ta bincike, sai suka sami wanda ake zargi dauke da kayan sarki da ta kalman jami’an soji, wukake da kuma wasu kayayyaki da ake zaton na tsafi ne, inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalibin Jami’ar jihar Akwa Ibom zai maka Makarantar a Kotu
Kazalika da aka tambaye shi wanda ake zargin ya ce, “zai kai kayayyakin ne zuwa garin Ogbomosho na jihar Oyo, inda daga bisani Kuma ya ce, kayan sarki da takalmar na dan uwan shi ne, wanda jami’in sojin kasar nan ne”, a cewar sa.
Hakan ya sa akayi gaggawar kame wanda ake zargin, inda kuma aka mika shi zuwa ofishin yan sandan dake Mokwa, domin cigaba da gudanar da bincike, inji Onyema Nwachukwu.