Daga Wakilin Dimokradiyya Usman Salisu Gurbin Mikiya
Rundunar Yansandan Jahar Katsina ta samu nasarar kama masu baiwa Yan ta’adda bayanan sirri, gami da Barayin Mashina da sauran masu laifi.
Kakakin Rundunar Yansandan Jahar Katsina SP Gambo Isah ya gabatar da masu laifin ga Yan Jarida, a madadin Kwamishinan Yansandan Jahar Sanusi Buba, a wani taro daya wakana a Shalkwatar Rundunar dake Katsina.
Haka Zalika, Rundunar Yansandan ta samu nasarar kama wani Kasurgumin Mai Laifi dake yin Sojan Gona sanye da Kayan Jami’an cibiyar gyaran akida, da Kuma mai yiwa Yara fyade, Wanda ya shahara wajen yin lalata da Kananan Yara, inda yayi da wasu guda biyu a Daura, gami Barayin Mashina da Dilolin su.
Acewar SP Gambo Isah, Rundunar ta samu nasarar kama Abdullahi Sani Mai Shekaru 40 dan asalin Garin Ruwan Godiya dake Faskari, da laifin bayarda bayanan sirri ga wani Kasurgumin Dan ta’adda Mai suna Ado Buji bayanda Al’ummar suka ji Yana waya dashi.
Acewar, Kasurgumin Dan ta’addan Ado Buji ya Kuma bashi Naira Dubu 800,000 domin ya sayo masu ababen more rayuwa, kari bisa ga gabatar da wani Malam Mustapha Mai shekaru 35 gareshi inda har ya bashi Naira Dubu 200,000.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yara Uku sun tsallake rijiya da baya a jihar Enugu
Kamar yadda yace, Rundunar Yansandan ta kuma cafke wasu Matasa da suka kasance manyan barayin Mashina, da suke satar mashinan Mutane a cikin garin Katsina, gami da masu sayen Mashinan.
SP Gambo Isah yace a kokarin da Rundunar take na yaki da ta’addanci da sauran ayyukan ashsha a Jahar, ta kuma samu nasarar kama wani Mai shiga irin ta Jami’an tsaro, inda bayan fitowar shi daga gidan yari da watanni biyu, ya saci mashina 8 kuma sanye da Kayan Jami’an Cibiyar Gyaran Akida ta Kasa a Katsina.
Kakakin Rundunar Yansandan yace, Sun Kuma samu nasarar cafke wani Aminu Isyaku Mai Shekaru 51 dake unguwar Makarantar Dadi primary a garin Daura, da laifin yiwa Yan mata biyu masu Kananan shekaru fyade.
Daga cikin Wanda ya yiwa fyaden akwai Wanda da’ita aka kai kudin Auren ta, inda dama an taba kama shi da irin wannan laifin.
A lokacin da aka bincike su, dukkanin masu laifin sun tabbatar da laifin da suka aikata, Kuma ana cigaba da bincike akan Lamarin.