‘Yan sanda a jihar Neja sun kama wani matashi dan shekara 24 Emmanuel Dominic a Minna wanda ya yi sojan gona, a matsayin jami’in soja domin a sako abokinsa dake hannun ‘yan sanda.
Da yake gabatar da wanda ake zargin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce, “Wanda ake zargin sanye da rigar sojan Najeriya, ya je sashin ‘yan sanda ya nuna kansa a matsayin sojan Najeriya mai lamba 05313 wanda yake aiki a TRADOC, Minna, domin a sako abokinsa dake tsare a hannun ‘yan sanda.”
Abiodun ya ce jami’an ‘yan sanda daga sashin Maitumbi ne suka kama wanda ake zargin da ke zaune a unguwar Tunga a Minna.
Ya ce a lokacin da ake yi masa tambayoyi, an gano wanda ake zargin sojan bogi ne wanda daga baya ya amsa cewa shi yaron bariki ne na Barikin Soja dake garin Minna, inda ya ce yasami rigar da yake amfani da ita ne daga mahaifinsa wanda ya ce soja ne.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce abubuwan da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da bindiga guda daya, gatari biyu, wuka guda daya, jakunkuna guda biyu, wando na OG kore guda biyu, rigar sojan daya, Takalmi, hular rufe fuska, da dai sauransu.
Hakazalika, rundunar ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata barna na taransfomar lantarki na garin Minna Babban birnin jihar ta Neja.
Abiodun ya ce an kama wadanda ake zargin ne a unguwar Lapai-Gwari da ke kan hanyar kasuwar kayan gini, Minna, ta hannun jami’an ‘yan sanda masu sintiri a yankin.
Ya ce a yayin da ake yi musu tambayoyi, an kama wasu mutane hudu a wurin da lamarin ya faru, inda suka amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa, kuma suka kai ‘yan sanda wurin wanda ya sayi igiyoyin wutar lantarkin da suka Sata.