By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Laraba ya bayar da kudi Naira miliyan 20 zuwa ga iyalan marigayi Brig.-Gen. Dzarma Zirkushu, wanda aka kashe a wata fafatawa tsakanin sojojin Najeriya da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.
Gwamnan ya bayar da umarnin gaggauta sakin asusun ne a lokacin da ya jagoranci tawagar jihar a ziyarar jaje ga iyalan Janar din daya rasu a unguwar Ribadu dake jihar Kaduna.
Mai magana da yawun Zulum, Isa Gusau, wanda ya tabbatar da cewa nan take aka fitar da asusun kamar yadda gwamnan ya umarce shi, yace an yi hakan ne don tallafa wa iyalan wadanda suka rasu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa za a kuma bayar da tallafin kudi ga sauran iyalan sojojin da suka mutu tare da Zirkushu.
Gusau yace gwamnan ya ziyarci iyalan Zirkushu tare da Sanatocin Borno uku, Kashim Shettima, Ali Ndume da Abubakar Kyari da shugaban jam’iyyar APC na jiha, Ali Dalori, da ‘yan majalisar wakilai biyu, Dakta Haruna Mshelia da Ahmad Jaha, da dai sauransu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gwamna Zulum ya jajantawa ‘yan uwa tare da bukatar su dasu jajanta wa wannan bajintar da marigayi Janar ya yi musu.
“Gwamnan yace al’ummar jihar Borno zasu ci gaba da godiya ga sadaukarwar marigayi Janar da sauran sojojin da suka mutu tare da shi, tare da wasu da dama da suka yi irin wannan sadaukarwa da kuma wadanda ke fagen daga a yanzu haka.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Kaduna ta kuma sanar da bayar da gudunmuwar naira miliyan biyu domin tallafawa iyalan marigayi Janar din.
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya sanar da bayar da tallafin jim kadan bayan gwamna Zulum ya saki kudin naira miliyan 20 ga iyalan.
Kazalika Aruwan yace tallafin da Kaduna ke bayarwa shi ne yabon Borno wajen tuntubar iyalan marigayi Janar din.