Kakakin dan takaran shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar wato Daniel Bwala ya ƙalubalanci Ministan birnin tarayya Abuja Mista Nyesom Wike kan matakin rusau don gyara tsarin birnin.
Bwala wanda ya kasance baƙo a cikin shirin Siyasarmu a Yau na gidan Talabijin ɗin Channels a ranar Alhamis ya ce akwai gagaruman ayyuka a gaban Wike da suka zarta rusau, wanda su ya kamata ya fi raja’a a kai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wike Ya Kalubalanci Duk Wanda Zai Dakatar Da Shi Daga PDP
Ya ƙara indai muddin da gaske tsarin birnin tarayya Abujan ake son gyarawa, roh ba kaɗai gidajen yaku bayi kawai za rusa ba, hatta fadar Aso Villa ita tana buƙatar a tasheta daga aiki.
“Birnin tarayya Abuja ba kamar ma’aikatar ayyuka ba ne, guri ne na gudanarwa. Akwai abubuwa da dama suka fi wannan rusau wanda su ya kamata a maida hankali a kai”
“Mu ɗauki misali da yadda ya ce yana so ya maida tsarin birnin tarayyar ne zuwa asalin yadda yake a baya, bari na gaya muku ita kanta fadar Aso Villa ma ba a kan tsari take ba son haka ita ya kamata a fara rusawa”
“Bugu da ƙari duk wani barikk soji da ka ganshi a birnin tarayya Abuja, ba a kan tsari yake, su ma ya kamata a rusa su.”
“Abu na gaba, ita unguwar Asokoro da kuke ji ana gwaɗata unguwar masu ƙumbar inda duk wani gwamna ko wani wanda ya isa yake da gina a wurin, ita ma ba a kan tsari take ba. Don haka dole a rusata.”
“Akwai ƙaddarorin gwamnati da dama wadanda kwata kwata ba a gjnasu bisa tsari ba”
Jigon na PDP ya ce Wike wanda tsohon gwamnan Jihar Rivers ne yana da zummar aiki tuƙuru, toh amma tilas ne ya bi abubuwan saɗɗa-saɗɗa muddin yana buƙatar cimma nasara ba wai kuma ta hanyar taƙala ba.
Idan za a iya tunawa dai a ranar 21 ga watan Agusta ne Wike ya sha alwashin gudanar da rusau a birnin tarayyar jim kaɗan bayan rantsuwar kama aiki.