Mahdi Mai dogon zamani shugaban ƙasar Kamaru ya naɗa sabbin hafsoshin sojin ƙasar kwana guda bayan kifar da gwamnatin farar hula a ƙasar Gabon.
Shugaba Paul Biya ya yi wani gagarumin garanbawul ne a majalisar hafsoshin sojin ƙasar a ranar Laraba da ta gabata.
KARANTA LABARIN NAN: Juyin Mulki A Afirika Ba Zai Yi Maganin Matsalarmu Ba -Atiku Abubakar
Kawo yanzu dai babu wani dalili daga shugaban ƙasar na ɗaukar wannan mataki.
Daraktan Sadarwar Ma’ akatar tsaron ƙasar Kanal Cyrille Guemo ya shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar Turkiya cewa tun ba yau ba shugaba Biya ya ƙudiri aniyar wannan sauye sauye.
Sai dai wani masanin harkokin tsaro David Otto ya bayyana cewa, guguwar juyin mulki da ta tashi a ƙasashe rainon faransa a baya bayannan na ɗaga hankali matuka wanda watakila hakan na daga cikin fargabar shugaban na Kamaru.
Ko da yake Mista Biya ya fuskanci ƙalubalen juyin mulki daga sojin ƙasar t0h amma bisa kokari da jajircewarsa hakarsu ta gaza cimma ruwa, inda yanzu haka ya maida sojin tamkar yan amshin shata.
Masana dai sun bayyana matakin Paul Biya na sauya hafsoshin tsaron kasar a matsayin barazana ga.mulkin farar da ba za su iya dakatar da kifar da mulkinsu ba.