Wata matar aure mai ɗauke da juna biyu ta mutu bayan mijinta ya kasa samo kuɗi a banki waɗanda zai biya domin a duba lafiyarta.
A cewar rahoton jaridar Legit.ng lamarin ya auku ne a Kasuwan Magani, cikin ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
KU KARANTA KUMA: Kasuwa tayi nauyi ko ciniki ba a samu yanzu ga kaya jibge a shago -Budurwa ta koka
Mijin matar, James Auta, ya bayyana yadda asibiti suka ƙi karɓar matar tasa saboda bai biya kuɗin da zaa duba ta saboda ƙarancin takardun kuɗin naira.
James Auta ya bayyana cewa:
“Na garzaya banki na domin na ciro kuɗi amma sai aka ce min babu kuɗi. Na koma ina neman masu POS, amma bam samu ko ɗaya ba saboda tunda aka fara wannan matsalar ta sababbin kuɗi, kusan mafi yawancin masu POS duk sun kulle shagunan su.”
Bayan ya kasa ciro kuɗi a banki, sai suka yanke shawarar su koma gida ko Allah zai sanya ta sauka lafiya.
Abin takaici shine lamarin sai ya ƙara ƙamari, inda matar ta mutu yayin da take ƙoƙarin haihuwa.
Matata ta fara naƙuda da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare. Tunda na kasa ciro kuɗi, sai na kira wata unguwar zoma a makwabtanmu. Amma matata na haihuwa, kawai sai jini ya ɓalle, duk ƙoƙarin da unguwar zoman tayi na tsayar da shi amma abin yaci tura.” Inji shi
Rashin Sababbin Kuɗi Ya Sanya Ƴan Najeriya Sun Koma Amfani da Kuɗin Nijar
A wani labarin na daban kuma, ƴan Najeriya sun koma amfani da ƙuɗaɗen ƙasar waje a dalilin rashin isassun sababbin kuɗi.
Ƴan Najeriya dake zaune a ƙauyukan dake kusa da iyakokin Najeriya sun koma yin cinikayya da kuɗin Cefa, kuɗin da ake amfani da su a ƙasashe rainon Faransa, yayin da ƙarancin sababbin kuɗaɗe na Naira ke ƙara ƙamari.
A cewar rahoton majiyar mu manoma da ƴan kasuwa a ƙauyukan Mfum, Gurin da Illella, a jihohin Cross River, Taraba da Sokoto, sun koma amfani da Cefa domin rage raɗaɗin da rashin sababbin kuɗin ya haifar.