By Abbas Yakubu Yaura
Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Ondo, Mista Oyediran Oyeyemi, ya kama aiki a hukumance a ranar Litinin inda ya yi alkawarin hada hannu da sauran hukumomin tsaro wajen yaki da rashin tsaro a fadin jihar.
Sabon CP yace rundunar sa za ta yi aiki da jami’an tsaro da aka santa dasu da sauran masu ruwa da tsaki a jihar a cikin tsarin dokar.
Da yake jawabi a ofishinsa dake unguwar Alagbaka a Akure, babban birnin jihar, Oyediran ya bayyana cewa yaje jihar ne domin tabbatar da cewa al’ummar jihar sun kwana da idanuwansu biyu.
Sannan yace cin zarafin dan Adam da ake zargin wasu jami’ai da aikatawa ba za a amince da shi a cikin umarninsa ba.
Sai dai ya lura cewa irin wannan lamari na cin zarafi ya ragu matuka.
Kazalika Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ya yi alkawarin ci gaba da horar da jami’an rundunar daga lokaci zuwa lokaci domin dakile irin wannan lamari.
Kwamishinan yace, “Idan muka yi la’akari da yadda jami’anmu ke cin zarafin bil’adama, zaku lura cewa an samu raguwar hakan so sai. Amma za mu ci gaba da yin bita da sake horar dasu har sai abin ya zama tarihi.”
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar dasu baiwa ‘yan sanda da duk jami’an tsaro da suka dace da bayanin duk wani yunkuri na shakku a yankunansu domin shiga lamarin cikin gaggawa.