By Abbas Yakubu Yaura
Al’ummar Fugar sun nuna damuwarsu kan lafiyar jami’in dan sanda reshen hukumar ‘yan sanda ta Fugar dake karamar hukumar Etsako ta tsakiya a jihar Edo, Mista Ibrahim Ishaq da aka sace.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa An yi garkuwa da Ishaq a makon daya gabata a kan tsohuwar hanyar Auchi-Ekperi-Agenebode yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa bakin aiki a Fugar.
Kungiyar hadin kan Fugar PU, a cikin wata sanarwa da kakakinta, Solomon Obomighie, ya fitar a ranar Lahadi, mai taken, ‘Sace jami’in dan sanda na Fugar, ya bayyana lamarin a matsayin daya daga cikin matsalolin rashin tsaro ba kawai a jihar Edo ba, har ma a fadin kasar baki daya.
Sannan sanarwar ta cigaba da cewa lamarin ya tabbatar da kiraye kirayen da ake yi na samar da tsaro a al’ummomi daban-daban, tare da yin nuni da cewa sace babban jami’in ya kara dagula al’amura a cikin al’umma.
Kungiyar ta ci gaba da cewa, “Sace DPO din ya fi daukar hankali saboda yana kara nuna tabarbarewar tsaro a kasar. Idan za a iya sace babban jami’in shari’a, waye kuma zai tsira?
“Muna yabawa rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa aikin ceton data kai kawo yanzu, muna kuma kira ga gwamnati data tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’armu.”
Comments 1