A jiya Asabar a gasar Firimiya ta Najeriya an fara fafata gasar ƙwallon hannu mai taken Prudent Energy Handball Premier ta ƙasar nan wato sabuwar kakar wasa kenan tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon hannu daban-daban dake fadin tarayyar ƙasar nan.
Gasar dai an fara ta data mata data maza a yau Asabar. A kakar wasan data gabata dai ƙungiyar ƙwallon hannu ta Kano Pillars ce ta zamo zakara. Amma kuma gashi an fara fafata sabuwar kakar wasa a yau.
Ga jerin wasannin da aka fafata a ɓangaren maza:
Coas Shooters sun buga walk over akan Borno spiders.
kada Stars 24 – 34 Lagos Seasiders.
Niger united 19 – 20 Kano Pillars.
D defenders 21 – 25 Safety Shooters.
Ga sakamakon ɓangaren mata kamar haka:
Defender Babes 26 – 28 Seasiders Babes of Lagos.
Imo grasshoppers 27 – 19 Kada Queen’s.
Edo Dynamos 29 – 27 Safety babes