A wanannn rana ta Lahadi an shiga rana ta 3 mai taken gasar share fage ta gwamnan jahar Katsina wato Masari. An fafata wasanni guda biyu a yau sannan kuma zuwa anjima da yamma za a sake fafata wasanni guda biyu.
Ga sakamakon wasannin da aka fafata daga safe zuwa yanzu:
Rarara F/C ta Lallasa Dadinkowa daci 2 da nema. Babangida Abubakar ne duka ya sami nasarar jefa ƙwallayen a dai-dai mintina na 80 da kuma 84.
Damburan tayi rashin nasara a hannun Zamfara United daci 3 da 1.
Za a fafata wasanni guda biyu a wannan yamnaci na Lahadi:
Katsina United da Sokoto United.
Plateau United zata fafata da Niger Tornadoes.
Wannan gasa dai gwamna Masari ya sanya tane domin nishadi da kuma sake hada kan al’umma baki daya. Ana fafata dukkanin wasannin a filin wasa na Mohammad Dikko dake birnin na jahar Katsina.