Daga: Abbas Yakubu Yaura
Sabon Sakatare-Janar mai zuwa na Ƙungiyar Ƙasashe Masu Tattalin Arzikin man fetur OPEC Mr. Haitham Al-Ghais yayi ta’aziyya rasuwar Mohammed Sanusi Barkindo.
A cikin sakon sa daya fitar a shafin Ƙungiyar na Twitter a ranar Laraba Mrs Al-Ghais ya rubuta cewa Barkindo ya jagoranci OPEC a lokacin da kasuwar Man Fetur a Duniya tayi kasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/gwamna-el-rufai-ya-%c6%99addamar-da-kwamitin-garga%c9%97i-a-kudancin-kaduna/
Al-Ghais ya rubuta cewa: “Babbar rawar da Barkimdo ya taka da gudummawar da ke da muhimmanci, tare da dogon tarihin tattaunawa da hadin gwiwa na kungiyarmu, sun sanya mu cikin wani yanayi mai karfi don ci gaba da tallafawa kwanciyar hankali da daidaito a kasuwar mai ta duniya”, in ji Al-Ghais.
Daga nan ne Sakatare Janar mai jiran gadon ya mika ta’aziyyarsa ga iyalansa, abokansa, abokan aikinsa, masoyansa da kuma kasarsa ta haihuwa Najeriya, da kuma daukacin Iyalan kungiyar OPEC.
Anyi jana’izar gawar marigayi Mohammed Sanusi Barkindo a Yola, babban birnin jihar Adamawa, cikin hawaye.
Ministan babban birnin tarayya, Muhammad Musa Bello ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana’izar.
A Wani Labarin Kuma ISWAP tace ita keda alhakin kai harin Kuje, ya saki bidiyo
Ƙungiyar Ƴan Ta’addan ISWAP tace ita keda alhakin kai harin gidan yarin Kuje inda aka saki Fursunonin wurin a Abuja.
Ƴan Ta’adda sun bayyana alhakin kai harin a cikin wani bidiyo da suka saki a daren ranar Laraba.
A cikin bidiyon, ƴan Ta’addan sun nuna yadda wasu daga cikin mambobin suka shiga gidan yarin Kuje.
Bidiyo mai daƙiƙa 38 ya nuna yadda ƴan ta’adda suka yi ta Harbe-Harbe kafin su samu damar shiga gidan yarin.
A dubawar da Majiyar mu tayi, ya nuna yadda ƙungiyar ta fara sakin bidiyon da larabci mai taken “Mayaƙan ISWAP sun kai hari a gidan yarin Kuje a jiya, kuma sun samu nasarar sakin fursunoni da yawa.”
Bidiyon ya nuna yadda Dattijai suke ta magana, inda suke bayyana ɗaukar alhakin kai harin da ƙona wurin.
Hukumar kula da Gidajen Gyaran Aƙidu na Ƙasa sun nuna cewa Fursunoni huɗu sun hallaka, a yayinda guda 879 suka tsere a lokacin kai harin.
Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar Mr Abubakar Umar a cikin sanarwar daya fitar yace maharan sun karya katangar gidan yarin, ta hanyar amfani da bam.
Ya kuma tabbatar cewa Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda Abba Kyari, da sauran manyan mutane basu tsere daga gidan yarin ba.