Daga Sulaiman Abubakar Dasume
Sallah ‘Daya Ce Daga Cikin Ibadun da Ubangiji Ya Wajabtawa Dukkan Musulmi Maza da Mata a Lokacin da Suka Kai Shekarun Balaga. Allah Ya Sanya ta Ta Zamo Rukuni Na Biyu Daga Cikin Rukunnan Musulunci Bayan Kalmar Shahada. Sallah Ita Wata Hanya ce Ta Ganawa Tsakanin Bawa da Ubangijinsa, Kuma Saboda Girmanta a Wurin Allah Ne Yasa Ubangiji Yace Babu Inda Bawa Yafi Kusantansa Kamar Lokacin da Bawan Yake Sujjadah. Hakika Manzon Allah (ﷺ) Ya Ambaci Sallah a Matsayin ginshiqin Addini Inda Yake Cewa:
“Kan Al’amari Shine Musulunci, Ginshiqinsa Kuma Shine Sallah, tsororuwar Tozonsa Kuma Shine Jihadi Saboda Allah”.
Ubangiji Ya Sanya wasu Daga Cikin Salloli Su Zamanto Wajibi Ne Ga Dukkan Musulmi, Kamar Sallolin Farillai Guda Biyar (Asubah, Azahar, La’asar, Magariba da Isha’i), Wasu Kuma Ya Sanyasu Su Zamo Sunnoni Kamar Sallar Jana’iza, Sallar Idi, Sallar Rokon Ruwa da Sallar Kisfewar Rana Ko Wata da Makamantansu.
ME AKE NUFI DA SALLAH?
Sallah a Yaren Larabci Tana Nufin Addu’a. Wasu Kuma Sunce Sallah Tana Nufin Girmamawa Ne.
Amma Sallah a Shari’ar Musulunci Tana Nufin Wasu Ayyuka Ne da Zantuka Ke6antattu, Wacce Ake Budeta da Kabbara, Ana Kulleta Kuma da Sallama Tare da Samuwar Niyya.
Amma Malaman Mazhabar Hanafiyya Sun Fassara Sallah da Cewa: “Ta Kunshi Wasu Ayyuka da Zantuka Ne Na Musamman, Kamar tsayuwa da Karatun Alqur’ani da Ruku’u da Sujjadah”.
SHARUDDAN KARBAN SALLAH
Kamar Sauran Ibadu, Sallah Tanada Sharuddan da Sai Bawa Ya Cikasu Sannan Sallah Take Wajabta a Gareshi. Sharuddan Sun Hada Da:
1. Musulunci: Sallah Bata Zama Kar6a66a Ga Wanda Ba Musulmi ba. Yana Daga Cikin Sharadin Kar6ar Sallar Bawa Shine Ya Zamanto Musulmi. Idan Kafiri Zai Shekara Yana Sallah Yayi Aikin Banza Domin Ubangiji Bazai Kalleshi ba Ma Balle Ya Bashi Ladan Sallar da Yakeyi.
2. Hankali: Sallah Bata Wajaba Ga Mahaukaci, Dole Sai Mutum Ya Zamanto Mai Lafiyayyen Hankali Sannan Sallah Take Wajaba a Gareshi.
3. Balaga: Hakanan Yaro Karami Wanda Bai Balaga Ba Sallah Bata Wajaba Akansa Har Sai Alamar Balaga ta Bayyana A Gareshi. Alamomin Sun Hada Da Cika Shekaru Goma Sha Biyar (15) Ga Da Namiji, Shekaru Sha Biyu (12) Ga Diya Mace. Ko Kuma Farayin Mafarki, Ko Fara Zuwan Jinin Haila Ga Mace, Ko Kuma Fitowar Gashin Hammata da Na Mara Ga Namiji da Macen. Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:
“An Dauke Alkaluma Ga Mutum Uku: Mai Bacci Har Sai Ya Farka, da Karamin Yaro Har Sai Ya Balaga, da Mahaukaci Har Sai Yayi Hankali”
Allah Ya Bamu Ikon Bauta Masa Yanda Yakeso.
Ameen