Tsohon dan Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ce bai kamata a kori babban limamin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari daga mukaminsa ba, saboda kalaman da ya yi kan kisan Deborah Samuel.
Idan dai za a iya tunawa, Limamin da ke kula da Masallacin kasa da ke Abuja, ya yi tsokaci kan kisan da aka yi wa Deborah, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sakkwato, mai mataki karatu aji na biyu wato 200level, wadda aka yi kashe a kan zargin cin zarafin Annabi Muhammad S.AW. ya ce musulmi suna da layin da bai kamata a ketare masu ba, Layin kuwa shine mutuncin fiyayyan halitta.
Wanda ya lashe kyautar Nobel a ranar Asabar, Farfesa Wole Soyinka ya yi kira da a kori Maqari kan wannan kalamai, bisa zargin cewa Maqari ya umurci magoya bayansa da su dauki doka a hannunsu.
Sai dai Shehu Sani, wanda guda daga cikin yan takarar gwamna a jihar Kaduna ya ce bai kamata a kama Maqari ba, yana mai cewa yana da hakkin bayyana ra’ayinsa.
Yan Takarar Shugaban Kasa Na Yankin Kudu Maso Gabas Na Ganawar Sirri
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar, tsohon dan Sanatan ya ce, “Kada a tsige Farfesa Ibrahim Maqari a matsayin babban limamin masallacin Abuja na kasa.
“Ya cancanci yafada ra’ayinsa a cikin dimokuradiyya. Haka kuma ko a baya na yi adawa da korar Sheikh Nuru Khalid daga nasa mukamin”.