Sama da mambobin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kogi 5000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
‘Yan jam’iyyar APC sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP ne a ranar Lahadin da ta gabata a unguwar Avrugo da makwabciyarta a karamar hukumar Igalamela/Odolu a jihar Kogi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za A Kammala Aikin Gadar Neja Ta Biyu A Cikin Shekarar 2024 – FG
Tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Igalamela/Odolu, Hon Collins’s Adama, wanda ya jagoranci sauran ‘ya’yan jam’iyyar zuwa PDP, ya ce APC ta gazawa ‘yan Najeriya.
A cewar sa, lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su zabi rashin shugabanci na gari a zaben 2023, yana mai jaddada cewa duk wani kuskure da aka yi a yanzu zai haifar da da mai ido ga al’ummar kasar.
Adama, wanda shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Igalamela/Odolu, Honarabul Attai Ndamusa Salifu da dan takarar majalisar dokokin jihar Hon Umar Zakito suka tarbe su a cikin ‘ya’yan jam’iyyar PDP, ya kuma ce jam’iyyar APC mai mulki a shirye take ta kwashe kayanta daga jihar Kogi har ma da matakin kasa.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kano Zata Samar Da Karin Kotuna 3 a Jihar
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na samar da karin wasu kotunan shari’ar Muslunci guda 3, bayan da kotun ta sauya wasu kotunan matsugunan daga ainihin inda suke a baya.
Batun sauya musu Matsugunin ya haifar da cece-kuce, inda wasu ke ganin cewa hakan wata dama ce ga gwamnatin na cefanar da ainihin wuraren da kotunan suke tun Fil’azal.