Sarkin Lafiya, tsohon mai shari’a Sidi Bage ya ce daga cikin abubuwan dake kawo rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya akwai matsalar ruwa.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya sauki manyan jami’an sojin da suke kwas na 42 a makarantar sojoji dake Jaji a fadarshi dake Lafiya.
Basaraken ya kara da cewa, rashin dazuka, wuraren kiwo da hanyoyin shanu suna taimaka wa wajen jawo rashin jituwar.
Bage ya ce, a zamanin da a masarautu ana kula da dazukan kuma hakan yana taimaka wa wajen kyautata muhalli.
Ya ce shirin Gwamnatin Tarayya na Agro Rangers zai taimaka sosai a wajen kawo zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.
Sarkin ya yi kira da sojojin da su yi amfani da sakamakon karatun nasu wajen kawo tsaro a kasar.
Kafin Sarkin ya fara jawabi, shugaban tawagar, Komado Hassan Idris-Alhaji ya ce sun zo jihar ne a ci gaba da bincike da suke kan rawar da kananan hukumomi suke bayarwa wajen tabbatar da tsaro a kasa.
Ya ce sarakunan gargajiya su ne kashin bayan zaman lafiya da tsaron Nijeriya
Ya kuma ce sun zo neman albarkan basaraken ne a matsayinshi na uba, ya taimaka musu da shawarwarin da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro.