Wata kyakkyawar budurwa ta gaji da zama babu saurayi inda ta fita neman abokin soyayya ɗauke da wani allo wanda ke nuna buƙatar ta na samun mashinshini. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
A wani bidiyo da ya yaɗu a manhajar TikTok, budurwar wacce ke sanye da jajayen kaya masu kyau waɗanda suka ƙara fito da kyawunta, akwai wani allo a saman kanta wanda aka rubuta ‘Bani da saurayi a shirye nake na samu mai sona’.
KU KARANTA KUMA: Barcelona ta bayyana gaskiya game da yiwuwar dawowar Messi kulob din
Budurwar tana ta murmushi abin ta kamar wata mai tallar kaya ga kwastomomi. Budurwar cikin rashin damuwa da irin kallon da mutane suke yi mata, tayi ta kewayawa ɗauke da allon a hannun ta.
Bidiyon nata ya ɗauki hankula sosai a yanar gizo. Wasu daga cikin waɗanda suka kalli bidiyo sun ɗauka cewa kawai ta fito neman suna ne yayin da wasu kuwa mamaki ne ya cika su yadda akai har budurwar ta iya yin hakan.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@@RMH ya rubuta:
“Hmmmm, wannan abin tsoro ne yadda samari suke wahalar samu yanzu.”
@MARCOUS ya rubuta:
“Daga UK nake, ki zo wajena nima banda budurwa kuma dama irin ki nake nema.”
@Reasonable ya rubuta:
“Kowane jinsi tsoron ɗayan jinsin yake yi yanzu, kowa so yake ya tsaya shi kaɗai, baya son rigima.”
@noagbehenkel12 ya rubuta:
“Daga wannan shekarar da muke ciki zuwa masu zuwa nan gaba, ƴanmata zasu fito neman samari kamar ba gobe.”