By Ishaq Dabai
Hukumar kula da sadarwa ta kasa NCC ta sanar da rufe dukkanin shafukan sadarwa na jihar Zamfara domin baiwa hukumomin tsaro damaryin aikin su dan dakile kalu balen tsaron jihar da take fama dashi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a yanke wannan hukuncin ne biyo bayan wata wasika da gwamnan ya aikewa da ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani a ranar 31 gawatan Agusta.
Shugaban hukumar farfesa Umar G. Danbatta shine ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a.
Wasikar tana mai cewa”an rufe dukkanin shafukan sadarwa na jihar zamfara dama jihohi dake makwaftaka da ita.
A cewar sanarwar ” kalubaken tsaron jihar Zamfara yayi kamari shi yasa aka dauki wannan mataki na rufe shafukan sadarwa na jihar daga yau 3 gawatan Satumba.
Kazalika sanarwar ta kara da cewa rufe shafukan sadarwar zai dauki tsawon makonni biyu, daga yau jumaa 3 ga watan satumba zuwa ranar 17 gawata.