Daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin majalisar dattawa Sanata Jibrin Barau na jam’iyyar APC ya karbi bakuncin zababbun sanatoci sama da 70 domin neman goyon bayansu gabanin kaddamar da majalisar wakilai ta 10 da za ta jagoranci majalisar dattawa.
Barau, wanda wannan shine karo na uku daya je zauren majalisar da ke wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwankwaso Ba Shugaban Kano Bane,Shine Buhari Na Gaba – Dan El-Rufa’i
Duk da cewa har yanzu bai fito fili ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar kujerar da ake nema ba, ya tura sojojin kafarsa domin ganawa da manyan masu ruwa da tsaki ciki har da manyan ‘yan majalisar tarayya.
A halin yanzu yana shugabantar kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa.
An tattaro cewa zababbun sanatoci sama da 70 ne suka halarci liyafar cin abincin rana da aka yi a otal din NICON da ke Abuja ranar Talata.
An gudanar da taron ne bayan gabatar da takardar shaidar cin zabe ga ‘yan majalisar.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, a ranar Talata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga akalla zababbun Sanatoci 98 a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja ranar Talata.
Jam’iyyun siyasa bakwai ne suka lashe kujerun ‘yan majalisar dattawa, inda APC ta samu rinjaye da kujeru 57.
Jam’iyyar PDP ta lashe kujeru 29; Jam’iyyar Labour shida; Jam’iyyar NNPP biyu; SDP, biyu; Jam’iyyar APGA da YPP, daya.
A wani labarin kuma, Kotu Ta Yi Wa Wasu Ƴaƴan Jam’iyyar PDP Ɗaurin Goro
Wata babbar kotun tarayya da ke Bauchi ta yanke wa wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP biyu a jihar Bauchi, Aminu Umar Gadiya da Saleh Hussaini Gamawa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari, bisa samun su da laifin hada baki da kuma karkatar da makudan kudaden haram Naira N142, 460,000.00.
Mai shari’a Hassan Dikko ya yankewa Gamawa da Gadiya hukunci ne a ranar 2 ga watan Maris, yayin da yake yanke hukunci kan tuhume-tuhume 2 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta shigar a kan wadanda ake kara.
Comments 1