A yammacin ranar Litinin din nan ne aka sanar da rasuwar Sanatan, wanda ya kawo adadin Sanatocin da suka rasu zuwa su hudu a majalisar dattijai yanzu haka.
Sanatocin da suka rasu kafin yanzu sun hada da Benjamin Umajunogu, Ignatius Longjan da Rose Oko, daga Disambar shekara ta 2019 zuwa Yuni shekara ta 2020.
Oshinowo, wanda yake wakiltar Gabashin Legasa, wannan shi ne karonsa na farko a majalisar dattijan ya rasu ne a yammacin ranar Litinin din nan da muke ciki.
Mamacin yayi dan majalisar jaha har tsawon sau hudu daga shekara ta 2003 zuwa 2019.
Sai dai a halin da ake ciki yanzu ba a bayyana dalilin rasuwar tasa ba, Amma dai rahotanni na nuna cewa Sanatan ya rasu ne a yau.