An samu fitowar jama’a da dama a wajen daurin auren fatiha diyar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau.
Kwankwaso ne Waliyyi, wanda ya baiwa Adamu Yusuf Maitama diyar tsohon Gwamna Halima Ibrahim Shekarau wacce akewa lakabi da (Amira).
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa daurin auren wanda ya gudana a masallacin Umar Bn Khattab da ke kan titin Zariya, ya samu halartar shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, Sanata Barau Jibrin da sauran manyan ‘yan siyasa.
Daruruwan magoya bayan manyan jam’iyyun siyasar jihar guda biyu ne suka halarci daurin auren, kowannensu na rera wakokin goyon bayan shugabanninsa, musamman ma ‘yan Kwankwasiyya da alamar jar hula ta mamaye wurin.
Yayin da Kwankwaso ya zarce gidansa bayan an daura auren, Shekarau ya kai shugaban majalisar dattawa zuwa gidansa, daga bisani kuma ya raka shi domin ta’aziyyar Kwankwaso bisa rasuwar kaninsa.
Idan za’a iya tunawa, a baya Shekarau ya ziyarci gidan Kwankwaso, a jiya Alhamis, don yi masa ta’aziyya.
Shekarau da Kwakwanso manyan ’yan siyasa ne ba Kano kadai ba har a fadin Najeriya baki daya.