Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya bayyana farin cikinsa da halartar taron aurin auren Yar Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bammali.
Wannan na cikin sakonsa na fatan alkhairi ga ma’auratan wanda ya aikewa Jaridar DIMOKURADIYYA a safiyar yau.
KARANTA HAKANAN Sanata Uba Sani Ya Bada Tallafin Miliyan 20 Ga Marasa Karfi
Sanata Uba Sani ya ce ya hadu da sarkin zazzau mai martaba Ahmad Nuhu Bammali tare da manyan mutane a wajen daurin auren yarsa Gimbiya Fatima Nuhu Bammali.
Sani ya ce “Na hadu da Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da sauran masu hannu da shuni a wajen daurin auren diyar sa, Gimbiya Fatima Nuhu Bamalli da angonta, Ahmed Audu Abubakar, wanda ya gudana jim kadan bayan kammala sallar Juma’a tare da al’ummar musulmi a karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna.
“Ina yiwa ma’auratan fatan Alheri da fatan Allah ya sanya musu mafificin alkhairi. Ameen“.
Duba kasa ga wasu hotuna
A Wani Labarin Kuma Zanga-zangar Karancin Man Fetur Da Kudi: Makinde Ya Tura Motocin Kyauta, Da Kayan Tallafi
Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde ya bayyana shirinsa na tura motocin bas na “Omituntun” zuwa manyan yankunan jihar domin ragewa mazauna Oyo wahalhalun da suke fama da shi na karancin man fetur da kuma sabbin kalubalen rashin kudin Naira.
Idan za a iya tunawa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu fusatattun matasa a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, suka gudanar da zanga-zanga tare da toshe hanyoyi, sakamakon karancin man fetur da kuma kudaden da ake samu a kasar, lamarin da ya janyo wahalhalu a makonnin da suka gabata.
Makinde, a cikin martanin da ya bayar game da bukatar jama’a, ya ba da umarnin dakatar da yakin neman zabensa don nuna goyon baya ga masu zanga-zangar ya kara da cewa gwamnati za ta ba da taimako don saukakawa mazauna Oyo daga ci gaba da wahala.
“Ya ku mutanen kirki na Jihar Oyo.