Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC Sanata Uba Sani, ya yi Allah-wadai da hare-haren wuce gona da iri da kuma lalata rayuka da dukiyoyi a kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Kajuru na jihar da wasu ‘yan bindiga suka yi.
Ya yi Allah-wadai da hakan ne a ranar Juma’a ta shafinsa na Facebook, inda ya ce dole ne hukumomin tsaro su yi kasa a gwiwa wajen gurfanar da masu aikata miyagun laifuka a gaban kotu.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Malami Da Ya Gwada Kwazonsa Da Wasu ‘Yan Mata Biyar A Katsina
“Labarin kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Kajuru abin bakin ciki ne kuma ina tare da Gwamna Nasir El-Rufai wajen mika ta’aziyyata ga wadanda suka rasa ‘yan uwansu a irin wannan mummunan lamari.”
“Haka kuma muna fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata cikin gaggawa,” ya rubuta.
Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kwamishinanta na tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan.
Idan dai za a iya tunawa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a wasu kauyukan kananan hukumomin Kajuru, Birnin-Gwari da kuma Giwa, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
A wani labarin kuma, An Cafke Mataimakin Shugaban Kasar Malawi Kan Zargin Karbar Cin Hancin Sama Da Dala 280,000
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Malawi ta bayyana cewa, an kama mataimakin shugaban kasar, Saulos Klaus Chilima tare da tuhumarsa da laifin almundahana kan badakalar cin hanci da ta shafi wani dan kasuwa dan kasar Malawi da Burtaniya.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce mataimakin shugaban kasar – wanda aka kwace iko da shi – an tuhume shi da laifuffuka da dama na cin hanci da rashawa da karbar cin hanci don yin tasiri a kan kwangilolin gwamnati.
Kakakin ACB, Egrita Mdala, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “Ya sami riba ta hanyar kudaden da suka kai dala 280,000 da sauran kayayyaki daga (dan kasuwan Burtaniya-Malawi) Zuneth Sattar,” don kamfanonin na karshen da za a ba su kwangilolin gwamnatin Malawi.