Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abeokuta, jihar Ogun ta kori dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a zaben 2023, Biyi Otegbeye, da kuma ‘yan takarar majalisar dokokin jam’iyyar a jihar.
An dai kori ’yan takarar ne bayan da bangaren jam’iyyar Labour reshen jihar Ogun suka tunkari kotu inda suka bukaci ta tilasta wa hukumar zabe ta kasa INEC kar ta amince da dan takarar gwamna da sauran su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani Ya Yi Allah-Wadai Da Kashe-kashen Kananan Hukumomi Uku Na Jihar Kaduna
Mai shari’a Akintayo Aluko wanda ya jagoranci shari’ar, ya tabbatar da cewa zaben fidda gwanin da ya samar da Otegbeye da sauran ‘yan takarar ba a bi dokar zabe ba wajen gudanar dashi.Daga nan ya soke zaben.
Yayin da Lauyan jam’iyyar Labour ya yaba da hukuncin, lauyan dan takarar ADC ya ce mai yiwuwa a tilasta musu daukaka kara kan hukuncin bayan samun damar yanke hukuncin kotun.
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Malami Da Ya Gwada Kwazonsa Da Wasu ‘Yan Mata Biyar A Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta damke wani malamin makaranta mai zaman kansa da laifin yin lalata da wasu yara mata guda biyar a ajinsa wadanda ya sha jawo su cikin bandaki domin yin lalata dasu.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah wanda ya gabatar da wanda ake zargin mai shekaru 25, Umar Isah a hedikwatar jihar a ranar Juma’a, binciken da suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya aikata hakan ga wasu yaran da ke daukar darasi a ajin sa.
Wanda ake zargin wanda ya amince da aikata laifin yayin da yake bayar da bayanin nasa na ikirarin ya ce: “A cikin ajin kamar falo ne mai karamin daki. Don haka sai na shigar da su cikin dan karamin daki daya bayan daya, in cire hijabinsu in yin lalata dasu”.