Sanatan jam’iyyar APC mai wakiltar Bauchi ta Arewa a majalissar dattijan Kasar nan, Adamu Bulkachuwa, ya ce da yawa daga cikin takwarorinsa sun goyi bayan yunkurin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da aka taso da wannan batu a majalissar.
Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata, jam’iyyar PDP a majalisar Dattawan ta baiwa shugaba Buhari wa’adin makonni shida da ya magance matsalar rashin tsaron da kasar nan ke fuskanta ko kuma a tsige shi daga kan mukamin nasa.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, Bulkachuwa ya ce barazanar tsige shugaba Buhari ita ce zabi na karshe kuma wajibi ne ga ‘yan majalisar.
Ya ce ‘yan majalisar sun yi kokari ta hanyoyi da dama don taimakawa bangaren zartarwa da kuma karawa shugaban kasa magance matsalar rashin tsaro a kasar nan, amma duk da hakan abun ya ci tura.
KARANTA WANNAN LABARIN: Peter Obi Ba Ya Goyon Bayan IPOB—Baba Ahmed
Tun da fari Elisha Abbo, wani dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC daga jihar Adamawa, ya fito fili ya goyi bayan shirin tsige Buhari, musamman ma ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP a majalisar dattawan.
Kalaman Bulkachuwa na zuwa ne kimanin kwanaki biyar bayan Sanatocin adawa, galibin Sanatocin Jam’iyar PDP da sauran takwarorinsu na wasu jam’iyyun siyasa, suka fice daga majalissar Dattawan.
Ficewarsu ta biyo bayan matakin da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yanke na yin watsi da kudirin su na tsige shugaban Kasa, da shugaban marasa rinjaye, Philip Aduda ya gabatar.
Da aka tambaye shi ko wa’adin makonni shida da aka baiwa shugaban kasar ya isa a shawo kan matsalar rashin tsaro a kasar nan???, Bulkachuwa ya yi fatan “shawo kan matsalar kafin cikar wa’adin”
Sai dai ya bayyana cewa, tun lokacin Buhari ya gana da hafsoshin tsaro da kuma wasu daga cikin jami’an tsaro, domin fatan samun sauye-sauye da dama.