Wani Dan Majalisar Wakilai Mai Suna Mista Musa Saidu Abdullahi wanda shine ya gabatar da kudirin dokar baiwa mata Musulmai damar sanya Hijabi a makaranta, ya gana da shugabannin Kungiyar Kiristoci ta Kasa wato CAN inda ya bayyana musu dalla dalla irin alfanun dake cikin dokar.
To sai dai Ƙungiyar ta nuna adawar ta a fili kan dokar, inda ta ce ai da ma tuni Akwai doka da ta baiwa ko wane dan kasa yancin yin abubuwan da suke so ciki har yancin Addini.
Da wannan hujja ce ya sa kungiyar ta CAN ta bukaci Dan Majalisar da ma Kwaryar Majalisa da su jingine wannan kudirin sun tunkari al’amauran da suka addabi kasar nan ciki har da na tsaro.
Dan Majalisar daga Jihar Neja Mai Wakilatar Mazabar Bida da Gbako da Katcha a majalisar tarayya ya mika Kudirin ne da zai rika kare hakkin cin zarafin addini, wanda kuma tuni da ma ya tsallake karatu na farko da na biyu.