By Abbas Yakubu yaura
Wata mata mai suna Blessing Omoru dake zaune a Agric Settlement, Esa-Oke, Jihar Osun, da aka sace tare da mijinta, Landan, ta sami ‘yanci.
An yi garkuwa da ma’auratan ne a gidansu dake Agric Settlement a ranar Larabar da ta gabata inda wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne suka yi garkuwa da su cikin daji inda rahotanni suka bayyana cewa sun shiga matsugunin nasu da wasu shanu kafin suyi garkuwar dasu.
An bayyana cewa, Blessing ta tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa dasu ne da sanyin safiyar Juma’a, inda aka gan su a Ijebu Jesa, bayan da wata tawagar data tsegunta lamarin ga masu gadin gandun dazuzzuka inda suka budewa wadanda suka yi garkuwa da su wuta.
A wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Asabar, Darakta Janar na Kiriji Heritage Defenders, Dokta Ademola Ekundayo, ya ce an samu Blessing ne bayan dare da wata tawagar da suka hada da mafarauta, mazan Kiriji Heritage Defenders da kuma hadin kan mutanen Oodua suka gano ta.
Ya ce, “Matar ta tsere kuma an ceto ta da safiyar yau a Ijebu Jesa. Har yanzu mijin yana tare da masu garkuwa da mutane, amma har zuwa yanzu ana ci gaba da neman mijin nata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ba a samu jin ta bakinsa ba, saboda kiran layin da aka yi masa bai shiga ba.