Hukumomin kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa; suna daukar ‘yan Nijeriya 424 duk shekara domin su yi karatu kyauta a jami’o’in kasar Saudiyya. Jakadan kasar Saudiyya a Nijeriya, Adnan Bostaji shi ne ya bayyana hakan a garin Kano a ranar Talata.
Jakadan ya bayyana hakan ne a wani taron kwana biyu da ya gudana a tsakanin masu ruwa da tsaki kan shirin bayar da ilimi kyauta a kananan makarantu da Sakandare na jihar Kano.
Bostaji ya ce wadanda suke
amfana da wannan shirin na hukumomin Saudiyya ana fito da su ne daga jihohi
daban-daban na Nijeriya, kuma suna karantar bangarori daban-daban na ilimi tun
daga matakin digiri na farko zuwa na biyu harda na uku ma.
Jakadan ya ce kaddamar da shirin bayar da ilimi kyauta a matakin Firamare da
Sakandare zai bunkasa bangaren ilimi a jihar Kano.