Wata yar Najeriya mai suna Okuneye Idris Olarenwaju wanda aka fi sani da Bobribsky ta tayar da hazo a dukkanin kafafen sada zumunta a yayin da take fadi game da abinda saurayin nata yake bata, gospelarea.com ta rawaito.
Bobribsky, ‘yar shekara 31 da haihuwa, ta wallafa ta shafinta na sada zumunta na Instagram kuma ta tambayi mutane nawa ne kudin da saurayinsu ke ba su a matsayin kudin ciyarwa a kowane wata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Budurwa ta Shararawa saurayin ta Mari, ta ƙi karɓar tayin Auren sa, ta buƙaci ya zage damtse
Bayan haka, ta bayyana cewa saurayin nata yana ba ta dala 7000 duk wata don ciyarwa, sannan kuma yana bata kudin gyaran gashi dala 5000 duk wata.
Kazalika ta kara da cewa yana bata kudin siyan man fetur da siyayyar sauran kayayyaki, wanda ya kai dala 5000 duk wata.
Bobribsky ta ci gaba da cewa idan mutumin da ba ya da yara ya kashe makudan kudi a kanta, ya kamata ta gode masa.
A WANI LABARIN KUMA: Kada ku sake ku mutu akan wani Ɗan Siyasa – Bishop Kukah
Bishop Matthew Kukah, Bishop na darikar Katolika na Diocese a Sokoto, ya shawarci magoya bayan ‘yan siyasa da kada su kashe kansu yayin da suke nuna goyon bayansu ga ‘yan takararsu.
Kukah ya bayyana cewa ’yan siyasan adawa abokai ne don haka bai kamata a dauke su da muhimmanci ba.
Kukah ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake gabatar da tambayoyi a shirin Rana na gidan Talabijin na Channels