Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kori Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Gabas, Albert Akpan, saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar YPP.
Wannan dai na zuwa ne bayan watanni bakwai da Ficewar sa daga PDP zuwa YPP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar INEC Ta Tsawaita Wa’adin Karbar Katunan Zabe
Akpan dai ya fice daga PDP ne a watan Yulin shekarar 2022 saboda rashin warware korafe-korafen zaben fidda gwani na gwamnan jihar Akwa Ibom.
Koda yake a kwanakin baya an yanke wa Mista Akpan hukunci tare da daure shi bisa laifin cin hanci da rashawa, korar tasa da kotu ta yi ba shi da alaka da hakan, jaridar Tribune Online ta rawaito.
Da take zartar da hukuncin, Mai shari’a Fadima Murtala Aminu, ta bayyana kujerar Sanata Akpan a matsayin wadda ba kowa, sannan ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta gudanar da zaben cike gurbi a cikin kwanaki 14, daga ranar 20 ga watan Janairu lokacin da aka yanke hukuncin.
“Saboda haka, wannan kotu mai girma ta tabbatar da cewa wanda ake kara na 1 Mr Akpan wanda ya yi murabus daga jam’iyya mai kara PDP amma ya kasa gudanar da aikinsa a gaban wannan kotu mai girma domin ya tabbatar da zargin da ake masa na rashin gaskiya da kuma bambance-bambancen da ake yi a cikin masu kara PDP. wanda ya sanya shi yin murabus ko sauya sheka zuwa jam’iyyar YPP.”
“Wanda ake kara na 1 ya sabawa sashe na 68(1) (g) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya shekarar 1999 ta hanyar kin barin kujerar sa a matsayin sanata a majalisar dattijai da aka samu a karkashin tallafin na mai kara,” in ji alkalin.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa korarren dan majalisar an umarce shi da ya biya zunzurutun kudin da ya kai Naira miliyan 5 ga jam’iyyar PDP wadda ta kai shi kara kan sauya sheka zuwa Jam’iyyar YPP.
A wani labarin kuma,Ancelotti Na Shirin Daukar Dzeko da Icardi zuwa Real Madrid
Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya bayyana tsohon dan wasan Manchester City Edin Dzeko da tsohon dan wasan gaba na Paris Saint-Germain Mauro Icardi a matsayin ‘yan wasan da zai dauka don karfafa gwiwar kungiyarsa.
A cewar El Nacional, Ancelotti yana so ya kawo Dzeko da Icardi zuwa Real Madrid don ƙarfafa kai hari, saboda Karim Benzema yana fama da rauni.