By Abbas Yakubu Yaura
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya yi alkawarin samar da sabbin sanya hannun jari a kasar Senegal a ranar Asabar, inda ya gabatar dasu a matsayin wani kari ga dimokuradiyya a wannan kasa da aka santa da kwanciyar hankali, a zangon karshe na rangadin da yake yi a Afirka.
Mista Blinken ya fada a ranar Asabar a babban birnin Senegal cewa, Afirka na iya samun tayin hadin gwiwa iri-iri, yayin da fafatawa tsakanin Amurka da Sin ke kara ruruwa, sabanin yadda ake kara cudanya da kasuwanci tsakanin kasashen Afirka da babbar kasuwar Asiya.
A ziyararsa a Senegal, Blinken ya rattaba hannu kan yarjeniyoyi ta biliyoyin daloli da kamfanonin Amurka, ciki har da kwangilar fasaha don ayyukan kare lafiyar jama’a da aikin inganta zirga-zirga tare da ingantattun hanyoyi.
Ya kuma ziyarci Cibiyar Pasteur dake Dakar inda ya yi alkawarin taimakawa ‘yan Afirka wajen yin musu alluran rigakafin.
“Wannan gaskiya ce mai sauki. Ba za mu yi nasara ba sai da jagorancin gwamnatoci, cibiyoyi da ‘yan kasar Afirka,” in ji Blinken.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Amurka ta kuduri aniyar karfafa hadin gwiwarmu a fadin nahiyar ta yadda za ta biya muradun jama’a a nan (a Afirka) da kuma biyan muradun mu,” in ji shi.