A safiyar yau litinin, masu Shaguna a kasuwar Aba da ke a cikin jihar Abia sun garkame shagunan su, saboda shari’ar jagorarn kungiyar tsagerun yan kabilar Inyamurai Nnamdi Kanu da ke fafutukar a raba Nijeriya.
An ruwaito daya daga cikin masu shagunan ya bayyana cewa, ba wai sun rufe shagunan, don goyon bayan Kanu ba, amma saboda su na jin tsoron za a iya samun barkewar rikici daga baya. Sai dai, harzu wa lokacin hada wannan rahoton, ba a riga an iso da Kanu kotun ba.
An gurfanar da shi ne a gaban babbar Kotun tarayya da ke Abuja, inda Mai Shari’a Binta Nyako ke jagoranta, bisa tumumar cin amanar kasa, inda daga baya, ya tsakele bilin sa da aka bayar kan cewa bai da lafiya a tun a shekarar 2017.
Sai dai, Kanu ya karya ta dukkanin ka’idojin belinsa da aka bayar, bayan da ya arce zuwa kasar waje.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abun da ya sa masana’antar fim ta wargaje, Shu’aibu Idris
An sake cafko Kanu a watan da ya gabata, inda jami’an tsaro na farin kaya wato, DSS suke tsare da shi a bisa umarnin kotu.