Wata mata cike da hawaye farinciki ta bayyana yadda diyarta ta siya mata dankareren gida, Legit.ng ta ruwaito.
Diyarta ta bayyana cewa shekaru tara kenan da aka yi muku korar wulakanci daga gida gado kuma mahaifiyarsu ita ta cigaba da daukar nauyin kulawa dasu.
KU KARANTA: An ɗaure wani sanata shekaru 42 a gidan yari kan cin hancin Miliyan 204
Bayan shekaru budurwar ta samu kudi kuma cike da sirri ta siya wa mahaifiyarsu gida mai kyau.
Bidiyon ya nuna yadda matar ba tare da saninta ba aka ja ta har gidan inda aka mika mata makullai.
Yadda tayi a bidiyon ya karya zuciyar mutane da dama. Yayin wallafa bidiyon a TikTok, @esther ta ce:
“Kun ga yadda na ba mahaifiyata mamaki ta hanyar siya mata gida. Na sanar da ita cewa na siya fili ne kuma yayana zai kai ta can don taga filin ba tare da ta san cewa kammalallen gida bane.
“Na ji dadin yadda na sanyata ciki farinciki. Kin cancanci fiye da haka mahaifiyata. Shekaru tara kenan da yayana wanda muke uba daya ya kore mu daga gidan gado.”
An Yankewa Tsohon Shugaban Jami’ar Zamfara Hukuncin Zaman Gidan Yari Shekaru 35 Kan Zambar N260m
A ranar Alhamis ne Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gabatar da farfesa Magaji Garba a gaban babbar kotun birnin tarayya, Garki dake Abuja, inda mai shari’a Maryam Hassan Aliyu ta same shi da laifuka biyar.
A cewar kakakin hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Wilson Uwujaren, an gurfanar da tsohon VC ne a ranar 12 ga watan Oktobar shekarar 2021, bisa zarginsa da karbar wasu kudade daga hannun wani dan kwangila bisa zargin bashi kwangilar Naira biliyan 3 kan shingen bangon jami’ar. .
Uwujaren ya bayyana cewa laifin ya sabawa sashe na 1 (1) (a) kuma ana hukunta shi a karkashin sashe na 1 (3) na dokar zamba da sauran laifuka masu alaka da zamba na shekarar 2006.