Daga Shuaibu Ibrahim Gusau
Wani jigo a jihar Zamfara kuma Dan jam’iyar APC ya yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai da ya kaurace wa siyasar jihar Zamfara, domin ba shi da wani iko, ko ‘yancin yin katsalandan a cikin abin da ke faruwa a jam’iyyar.
Daya daga cikin jigo a siyasar jihar, kuma wanda yabi gwamnan jihar wajan sauya sheka daga jam’iyar APGA mai alamar zakara, zuwa jam’iyar APC, ya bayyana haka ga manema labarai a Daren jiya, a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Ya kara da cewa “Ya kamata gwamna El-Rufai ya dai-na hada baki da Abdul’aziz Yari da sanata Kabiru Garba Marafa, don haifar da rudani a siyasar jiharZamfara, ya ce “Ya kamata El-Rufai ya san cewa, muna kaunar sa domin shi surikin mu ne, kuma muna yi masa fatan alheri ko da yaushe, don haka ya kamata ya dai-na taimaka wa wajen haifar da kiyayya a cikin jam’iyar mu da jihar mu,” in ji shi.
Ya kara da cewa, gwamnan jihar Kaduna Nasiru El -Rufa’i, “Tun da ake kashe mutane a jihar Zamfara, be taba zuwa da sunan jajantawa ba, don haka hawainiyarsa ta kiyayi jihar Zamfara, ya tsaya cen yamagance matsalarsa” inji shi
KARANTA WANNAN LABARIN: Yari da Marafa Sun kunno wuta kan kan baiwa Matawalle jagorancin APC
Shinkafi ya yi kira ga mutanen jihar, da kar su yarda a yaudare su, da ‘yan siyasa masu yada jita-jita game da yanayin siyasa a jihar.
Ya ce “Ya kamata dukkanmu, mu hadu ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, don bayar da gudummawar mu ga ci gaban jihar Zamfara,” in ji shi.