Shugaban kasa Buhari ya nada tsohon tauraron kwallon kafar kasar, Daniel Amokachi a matsayin mai taimaka masa kan harkokin wasanni.
Ministan wasanni, Sunday Dare ya sanar da nadin sakamakon wasikar da Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ya rubuta wadda ta bayyana amincewar shugaban kasa na bai wa Amokachi mukamin.
Wasikar da aka aikewa Amokachi, ta ce Buhari na farin cikin sanar da shi nadin da aka masa na mai taimaka masa kan harkokin wasanni daga ranar 11 ga wannan wata na Agusta.