Daga: Abbas Yakubu Yaura
Fadar shugaban kasa ta sanar da nadin Honorabul Nasiru Baballe Ila a matsayin sabon mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar wakilai ta kasa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasa ya sanya wa hannu, ta ce Buhari ya amince da nadin Hon Nasiru, wanda ya fito ne daga kwalejin Victory ta Alexandria da West London College da ke kasar Ingila.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/zaben-fidda-gwanin-shugaban-kasa-na-apc-wakilan-da-suka-karbi-kudi-yanzu-haka-suna-nadama-amaechi/
Fadar shugaban kasa ta bayyana Nasiru a matsayin hamshakin dan kasuwa mai sha’awar sha’anin safarar kaya da sana’ar fata kafin ya shiga harkokin siyasa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa a shekarar 2011 zuwa 2015, an zabi Nasiru a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tarauni a Kano.
Yanzu ya maye gurbin Hon.Umar Ibrahim El-Yakub wanda shugaban kasa ya nada minista.
A Wani Labarin Kuma Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wadanda suka kada kuri’a a jam’iyyar APC a zaben fidda gwani na shugaban kasa yanzu haka suna yin nadamar shawarar da suka yanke.
Amaechi ya ce wakilan da suka bari kudi suka yi tasiri a kan shawarar da suka yanke a lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa yanzu haka suna nadama.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana haka ne a yayin bikin cika shekaru 60 da haihuwa na Apostle Eugene Ogu, Janar Overseer na Abundant Life Evangel Mission, a karshen mako a garin Fatakwal na jihar Ribas.
Ya yi nuni da cewa sanya kudi don samun kuri’u ba zai magance matsalolin Najeriya ba.
Amaechi ya kuma bukaci bayin Allah da su yi wa talakawan Najeriya addu’a domin su zabi shugaban da zai magance matsalolin kasar.
A cewar Amaechi: “Wadanda suka kada kuri’a a zaben fidda gwani na APC, su waye? Su talakawan Najeriya ne. Kudaden da suka samu sun warware musu matsalar nan take, yanzu suna cewa sun yi kuskure, yanzu kuna jin abubuwa daban-daban.
“Idan kuna yi mana addu’a, ga shugabancin kasar nan, amma kuma ku yi wa talakawan Najeriya addu’a domin su zabi shugaban da ya dace ya shugabanci kasar nan.
“Ba da kudi ba shine mafita ga matsalar Najeriya ba. Maganin matsalar Najeriya ita ce dukkan ku dole ne ku tashi.”
A yayin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC a Abuja, Amaechi ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar, Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Ribas ya zo na biyu bayan Tinubu wanda ya samu mafi yawan kuri’u.
Rahotanni sun bayyana cewa zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya barke ne sakamakon sayen kuri’u.