Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Dakta Fatima Waziri-Azi a matsayin Babbar Daraktar hukumar yaki da saffarar bil-Adama ta kasa.
Babban Mai taimaka Shugaban kasa akan kafafen yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, Kuma yai mata lakabi da” Shugaban kasa Buhari ya nada Fatima Waziri Azi a matsayin Shugabar Hukumar NAPTIP”
A cewar sanarwar, An nada ta ne biyo bayan shawarar da Ministar bada agaji da magance iftila’i Sadiya Farouq ta badayar, wacce ta ce, ” A kwai bukatar hukumar NAPTIP ta kara azama, domin samun manyan nasarorin a aiyukan ta”
KARANTA WANNAN. LAABRIN: Yadda Sanata Uba Sani ya taimaki al’umar Mazabar shi
Waziri-Azi tsohuwar shugaba ce a Sashin shari’a na Cibiyar Nazarin Shari’a ta Najeriya, mai fafutukar kare hakkin mata, Kuma Mai yaki da cin zarafin matan aure, kazalika kwararriya ce a fannin Shari’a.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnatin Jahar Imo ta gargadi yayan Kungiyar kafa kasar Biafra, data guji aikata ayyukan ta, a lokacin ziyarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Ana saran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Hope Uzodinma yayi a ranar Alhamis.
Kungiyar IPOB ta aiyana dokar zaman gida a ranar Alhamis, tana mai gargadin cewa, ba’a bukatar zuwan Shugaban Kasa a dukkanin yankin Kudu maso Gabas.
Amma Kwamishinan Yada Labaru da Dabaru Declan Emelumba Wanda yayi jawabi ga Manema Labaru a Owerri, yayi gargadin cewa, Babu wani mutum da zai shiga matsayar da Gwamnatin ta cimmawa akan zuwan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Yace “banji wata dokar zaman gida daga wata Kungiya ba. Ina tunanin Wanda naji shine wasu suna so a sako masu Shugaban su, Kuma zasuyi Zanga-zanga duk ranar daya bayyana a kotu.
“Amma Muna magana ne akan zuwan Shugaban Kasa. Shugaban Kasa na gudanar da ziyara a Imo, Kuma zamuyi dukkanin abinda zamu iya, domin hana gudanar da wani mummunan abu. Mun yi dukkanin shiri na Jami’an tsaro, Kuma Ina tabbatar maku dacewa, mutanen Imo suna cike da murnar zuwan Buhari.
Emelumba ya bayyana ziyarar Shugaban Kasa a matsayin ta hadin kai, domin itace ta farko da Shugaban ƙasa zai kai ziyara domin kaddamar da wasu ayyuka.
Kwamishinan yace Mazauna Jahar sun kagara su karbi Shugaban Kasa, domin nuna haka, ya sanya suka kulle dukkanin kasuwanni a ranar Alhamis.