Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Aminu Umar-Sadiq a matsayin sabon Manajan Darakta na Hukumar Kula da Zuba Jari ta Najeriya NSIA.
Bayanan hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa ga ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Tanko Abdullahi, ya fitar a daren jiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Da Ya Sa Na Yi Murabus Daga Matsayin Shugaban BoT Na PDP – Jibrin
A cewar sa, nadin ya biyo bayan cikar wa’adin Mista Uche Orji.
Ya ce, “Nadin sabon shugaban ya biyo bayan cikar wa’adin tsohon shugaban, Mista Uche Orji, wanda wa’adinsa ya kare ne a ranar 30 ga watan Satumba, 2022 bayan ya yi wa’adi biyu na shekaru biyar, bayan nadinsa a ranar 2 ga watan Oktobar shekarar 2012.”
An kuma nada manyan Daraktoci guda biyu. Sun kasance: Mista Kolawole Owodunni, Babban Darakta, da Misis Bisi Makoju, Babbar Darakta, ta NSIA baki daya.
Sashe na 16 (3) na Dokar Kafa NSIA na shekarar 2011 ya ƙayyade cewa za a kafa Kwamitin Zaɓuɓɓuka (ENC) don fara aiwatar da tsarin daukar ma’aikata da zaɓe don maye gurbin Mista Orji, MD, da Daraktocin Gudanarwa.
Aminu Umar-Sadiq, wanda a halin yanzu babban Darakta ne kuma shugaban sashen samar da ababen more rayuwa, ya yi digirinsa na farko da na biyu a fannin Injiniya a Jami’ar Oxford (Saint John’s College), Oxford, United Kingdom (UK).sannan w Archbishop Tutu Leadership Fellow (UK). ATLF) da kuma Mandela Washington Fellowship (MWF).
Umar-Sadiq ya fara sana’ar sa a Mergers and Acquisitions M&A) ya mai da hankali kan Infrastructure and Energy a Bankin zuba jari na Morgan Stanley, inda ya wuce zuwa Infrastructure mayar da hankali ga kamfanoni masu zaman kansu a Denham Capital Management, duk a Burtaniya.
Ya yi ayyuka da dama da suka hada da Presidential Fertiliser Initiative, shirin sauya shigo da kayayyaki masu inganci miliyan 1, mai rahusa ga manoma a farashi mai rahusa metric ton na taki. Har ila yau, ya kasance wani bangare na asusun bunkasa ababen more rayuwa na shugaban kasa, asusun zuba jari da ya mayar da hankali kan aiwatar da manyan ayyuka guda biyar na kasa baki daya a fannin sufuri da wutar lantarki.
Yana da gogewa sosai a fannin zuba jari da masana’antar ababen more rayuwa.
Misis Bisi Makoju kwararriya ce ta fannin Kudi da gogewa mai yawa, a fannin kula da hada-hadar kudi, yayin da Mista Kolawole Owodunni kwararre ne da ya shafe shekaru 18 yana aiki a Sashin Sabis na Kudi tare da mai da hankali kan sarrafa zuba jari, Gudanar da Hatsari da Baitulmali. Ana sa ran dukkansu za su taimaka wajen tafiyar da harkokin zuba jari da samar da ababen more rayuwa da kuma ciyar da fannin zuwa wani babban tudu.
A wani labarin kuma, Wasu ‘Yan Uwa 9 Sun Yi Mutuwar Ban Mamaki A Jihar Kogi
A karo na biyu cikin kwanaki, wasu ‘yan uwa tara ne suka mutu a wani lamari mai abin ban mamaki a jihar Kogi.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a garin Nagazi da ke karkashin karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi