Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nada uwargida Dakta Folashade Yemi-Esan a matsayin mukaddashiyyar shugabar hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya (HFCS).
A sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar a shafinta na Twitter a daren ranar Laraba, ta ce nadin Uwargida Dakta Folashade ya fara aiki nan take, ba tare da bata lokaci ba. Sanarwar ta kara da cewa Dakta Folashade, wacce babbar Sakatariya ce a ma’aikatar albarkatun man fetur, za ta maye gurbin uwargida Winifred Oyo-ita, wacce aka umarta ta tafi hutun dole mara lokaci domin bai wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC kammala binciken da ta fara a kanta.
Haka zalika, shugaba Buhari ya amince da yin karin wa’adin ritayar wasu manyan Sakatarorin gwamnatin tarayya guda bakwai na tsawon shekara guda, wanda zai fara daga ranar 1 ga watan Oktoba.
Fadar shugaban kasa ta ce an kara wa manyan Sakatarorin wa’adi ne domin tabbatar da ganin gwamnatin shugaba Buhari ta cimma manufofinta guda 9 da kuma bawa sabbin ministocin da aka nada damar kai gaci.
Manyan Sakatarorin da aka kara wa wa’adin barin aiki sun hada da: Uwargida Georgina Ehuriah ta Ma’aikatar harkokin cikin gida, Uwargida Ifeoma I. Anagbogu ta Ma’aikatar harkokin mata, sai Uwargida Grace Gekpe ta Ma’aikatar yada labarai da al’adu da kuma Dakta Umar M. Bello na Ma’aikatar noma da raya karkara, sai Suleiman Mustapha Lawal na Ma’aikatar harkokin waje da kuma Uwargida Comfort C. Ekaro dake Ma’aikatar albarkatun ruwa, sai na karshe Mista Olusegun A. Adekunle a Ofishin Sakataren gwamnatin tarayya.