By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga birnin tarayya Abuja domin zuwa halartar taron shugabannin kasashen Afirka da za’a gudanar a Malabo na kasar Equatorial Guinea da zai maida hankali musamman kan harkokin tsaro.
Wata sanarwa da mai taimaka wa Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar ta ce taron na kwanaki uku da za a yi a tsakanin ranakun 26 zuwa 28 ga watan Mayu, zai kuma mai da hankali kan kalubalen jin kai a Afirka, da batutuwan da suka shafi ’yan gudun hijira, da wadanda aka maido dasu gida.
DUBA WANNAN LABARIN: NECO: Jami’an ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Ma’aurata Bisa Damfarar Wasu Mutane Sama 50
A gun taron, shugabannin kasashen Afirka za su duba batun ta’addanci da sauyin gwamnati da ba a bisa ka’ida ba, tare da kara tabarbarewar hakin bil’adama da tattalin arziki.
Buhari zai bi sahun shugabannin kasashe da gwamnatoci don tattaunawa kan kalubalen jin kai a Afirka, da kuma halartar taron amincewa da taron Majalisar Dinkin Duniya kan ayyukan jin kai da kuma alkawuran taron.
Dangane da batun tsaro da gudanar da mulki, Majalisar shugabannin kasashen Afirka za ta dauki matsaya daya kan ta’addanci da sauyin gwamnati da ba bisa ka’ida ba, tare da cimma matsaya kan sabbin hanyoyin dakile matsalar.
Haka kuma shugaba Buhari zai gana da wasu shugabannin na Afirka yayin ganawar a Malabo.
Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, wacce ita ce shugabar kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka, na tare da mijinta don zuwa wajen taron kungiyar Tarayyar Afirka.
Shugaban kasar zai kuma samu rakiyar ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan Tsaro, Maj-Gen Bashir Salihi Magashi (mai ritaya); Ministan jin kai da kula da bala’oi da cigaban al’umma Sadiya Umar Farouq; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj-Gen Babagana Monguno (mai ritaya).
Sauran sun hada da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da shugaban hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) Abike Dabiri-Erewa.
Comments 1