Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya NSCDC guda bakwai da ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a jihar Kaduna a lokacin da suke bakin aiki.
A cewar wata sanarwa da Garba Shehu, babban mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, ya fitar a ranar Alhamis, yayin da yake bayyana alhininsa game da rasuwar, shugaban ya bayyana rashin jami’an NSCDC a matsayin wani lamari mai ban tausayi tare da jinjinawa jajircewar mutanen da suka sadaukar da rayukansu ga al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kakakin PDP Na Gombe Ya Koma Jam’iyyar NNPP
Ya ce: “Jami’an NSCDC da suka jajirce wajen ganin sun kare al’ummarmu sun yi sadaukarwa sosai wajen gudanar da ayyukansu.
“Tunanina yana tare da iyalan wadanda suka mutu da kuma ’yan uwansu a hidimar. Allah Madaukakin Sarki Ya ba daukacin ma’aikata karfin gwuiwar jure rashin.”
Shugaban ya umurci rundunar da su nemi ‘yan fashin da suka haddasa wannan hasarar tare da biyansu farashi.
A wani labarin kuma, WHO Ta Ankarar Kan Amfani Da Wani Maganin Tari
Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadi game da amfani da maganin tari na Indiya guda biyu ga yara da ake kan karkara a Uzbekistan. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
WHO ta ce magungunan, wanda Marion Biotech ya kera, “na da karancin inganci” kuma kamfanin ya gaza bayar da tabbacin kare lafiyarsu.