By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da rahoton kisan kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina, Dakta Rabe Nasir da aka yi a yammacin ranar Alhamis.
Shugaban a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a yammacin ranar Alhamis, ya bayyana kisan kwamishinan a matsayin wani mummunan aiki da Allah wadai da shi, inda ya kara da cewa “babu inda za a yi irin wannan tashin hankali a kasarmu.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shugaban yace ya ji takaicin kisan gillar da aka yi wa wannan shugaba mai tasowa wanda ya yi wa al’ummarsa da jiharsa da kasa hidima da kwazonsa.
“Tunanina sa yana tare da dangin da suka rasu,” in ji shugaban.
Ya bukaci jami’an tsaro dasu yi cikakken bincike tare da gurfanar da wadanda ke da hannu wajen aikata wannan mummunan laifin.